Kawo yanzu akwai daruruwan yan gudun hijira da tashe tashen hankula suka raba da gidajensu, wanda yanzu haka suke watse a wani sansanin da aka tanadar a yankin mutum biyu, baya ga wadanda ke gudun hijira a wasu jihohin dake makwabtaka da jihar.
Jama’a da dama ne ke gudun hijira a jihar Taraba, sakamakon tashe tashen hankulan da aka fuskanta a wasu sassan jihar, rikicin dake da nasaba da kabilanci ko addini.
A ziyarar Ministan harkokin mata da kuma walwalar jama’a Sanata Hajiya Jummai Alhassan, zuwa sansanin wucin gadi da aka tanadar ga ‘yan gudun hijira a yankin Mutum Biyu, ‘yan gudun hijirar sun bayyana mata matsalolin da suke fuskanta, wanda suka hada da rashin ruwa da bayan gida.
Ministar tace ta zo jihar ne domin ganin halin da ‘yan gudun hijirar ke ciki kamar irin yadda takai ziyara a jihohin Borno da Adamawa, inda ma ta bayyana musu sakon shugaba Buhari, na cewa ya shirya wani ofis karkashin ofishin sakataren gwamnati don lura da harkokin ‘yan gudun hijira a Najeriya.
Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.