NIAMEY, NIGER - A karshen wani taron da ya hada jami’an gwamnatocin kasashen biyu a makon jiya, bangarorin sun yanke shawarar kara jan damara don ganin an cimma gurin da aka sa gaba kafin shudewar wa’adin da aka kayyade kamar yadda mataimakin sakataren hukumar hadin gwiwar Nijar da Najeriya, Alhaji Adamou Namata, ya bayyana wa manema labarai.
Mataimakin sakataren hukumar hadin gwiwar Nijar da Najeriya Joint Commission, Alhaji Adamou Namata, wanda ya halarci taron ministocin sufurin kasashen biyu a Abuja, na wannan bayani ne bayan da shi da ministan sufurin Nijar, Alma Oumarou, suka yi wa shugaban kasa Mohamed Bazoum bayanin abubuwan da aka tsayar a yayin wannan zama.
Wannan wani yunkuri ne da ke hangen bunkasa harakokin kasuwanci da jigilar kaya a tsakanin Najeriya da Nijar.
A shekarar 2018 ne gwamnatocin Nijar da Najeriya suka kudiri aniyar shimfida layin dogo daga Kano mai ratsawa wasu sassan Jihar Katsina zuwa Maradi, a matsayin wata hanyar bai wa ‘yan kasuwar kasashen biyu damar hada hada da tashar jiragen ruwan Lagos. Biliyan biyu na dalar Amurka ne ake bukata domin kammala wannan aiki.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5