Hukumar yaki da safarar mutane ta Najeriya NAPTIP ta koka bisa yadda masu safarar mutane ke ta kai ‘yan mata kasar Jamhuriyar Turkawan arewacin Cyprus, inda suke karewa cikin ayyukan karuwanci ko bauta.
Wata sanarwar hadin gwiwa da hukumar da kuma wata kungiyar kare hakkin dan adam ta arewacin Cyprus din suka aikewa Sashen Hausa na Muryar Amurka ta nuna cewa ana yaudarar ‘yan matan ne ta hanyar kwadaitar dasu cewa ko dai za’a sama masu guraben karatu ko aikin yi, amma daga bisa sai a sami akasi.
Alkaluman binciken da kungiyar kare hakkin bil'adaman ta arewacin jamhuriyar Turkawan Cyprus din ta gabatar ya nuna kusan kashi saba'in cikin dari na matan da ake safararsu zuwa kasar daga Najeriya ne kuma suna karewa ne cikin harkar karuwanci.
A dai watan Maris din shekara ta dubu biyu da ashirin, hukumomi sun mai da safarar mutane a matsayin babban Laifi to amma basa kazar kazar wajen daukar batun da muhimmanci.
Koda ma dai an samu kubutar da wadanda aka yi safarsu din to ba mai bi masu hakki kuma ba wani dauki da suke samu daga mahukunta kasancewar har yanzu ba a tsara wasu dokoki da zasu sa kafar wando daya da masu fataucin bil'adaman.
Wani malamin jami'a a Najeriya da ya yi karatun babban digiri a can Cyprus, Muhammad Alhaji Adamu, ya shaidawa Muryar Amjurka cewa kasar wacce a duk duniya kasar Turkiyya ce kadai ta aminta da ita a matsayin kasa mai 'yanci tana da rauni wajen bin ka'idoji da dokoki, kuma kofofinta a bude suke ga 'yan Najeriya inda su kuma idan sun je suke cin karensu babu babbaka.
Shima mai rajin kare hakkin bil'adama Kwamared kabiru sa'idu Dakata ya nemi gwamnati da tayi abin da ya dace wajen ganin an shawo kan wannan matsala sannan ya shaidawa matasan cewa ganin kiytse suke wa rogo.
Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina:
Your browser doesn’t support HTML5