Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Damke Wasu Hamshakan Masu Safarar Bakin Haure a Nijer


Wasu bakin haure da su ka doshi Libiya daga Agadez, Jamhuriyar Nijer
Wasu bakin haure da su ka doshi Libiya daga Agadez, Jamhuriyar Nijer

Yayin da masu fataucin bakin haure ke dada yawa a Jamhuriyar Nijer, hukumomi sun tashin haikan wajen dakile wannan sana’a ta ratsawa kasar Nijer da bakin haure masu niyyar zuwa kasashen ketare. A baya bayan nan hukumomi sun kama hudu daga cikin shahararrun masu fasakwabrin bakin hauren. Hukumar ‘yan sanda ta ce mutane hudun da aka kama, su daga cikin masu ratsa kasar Nijer da bakin haure masu niyyar zuwa wasu kasashe na arewacin Afurka.

Ana alakanta yawaitar wannan sana’ar da rashin ayyukan yi musamman ma tsakanin matasa, wadanda talaucin da su ke fama da shi ya sa ba su daddara duk kuwa da tsauraran matakan da ake daukawa kan masu wannan haramtacciyar sana’ar. Ahmadu Umaru, shugaban tsoffin masu safarar bakin haure, ya ce masu wannan sana’ar akwai su a dukkan jahohin Nijer kuma su na abokan hulda a kasashen da ke kewaye da Nijer. Don haka, a cewarsa, show kan wannan mugunyar sana’a ba abu mai sauki ba ne.

Tun bayan da kasashen yammacin duniya su ka bai wa Jamhuriyar Nijer wasu kudaden tallafi don ta taimaka wajen hana masu ratsawa cikinta su na fataucin bakin haure, kasar ta kara kaimi wajen yaki da fasakwabrin bakin hauren, wanda don haka wasunsu su ka daina. Amma sannu a hankali, sai wasu daga cikinsu su ka sake shiga wannan sana’ar saboda talauci. Malam Abdulkarim ya ce akasarin masu wannan sana’ar matasa ne, wadanda a maimakon su shiga sace sace ko kashe kashe da sauran manyan laifuka, su ka gwammace yin wannan sana’ar.

Don haka, malam Abdulkarim ya yi kira ga gwamnatin Jamhuriyar Nijer da ta samar ma matasa mafita muddun ana so a daina wannan haramtacciyar sana’ar. Mafitar kuma, a cewarsa, ba ta wuce ayyukan yi ba. To saidai wasu na ganin idan aka kara tsaurin matakan da ake daukawa, za a samu saukin al’amarin.

Saurari cikakken rahoton Hamid Mahmud:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG