NAJERIYA: Bulaguro Zuwa Amurka Bai Zama Wajibi Ba

Jirgin kamfanin American airline.

Gwamantin Najeriya ta shawarci ‘yan kasar da su dakatar da bulaguron da suke shirin yi zuwa Amurka, har sai an fahimci inda manufofin shugaba Donald Trump kan baki ya sa gaba.

Cikin wata sanarwa da aka fitar daga babbar mai taimakawa shugaban Najeriya kan al’amuran da suka shafi kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa, ta shawarci ‘yan Najeriya da cewa yin bulaguronsu zuwa Amurka bai zama wajibi ba, da su dakata har sai an fahimci tarnakin dake tattare da manufofin gwamnatin Donald Trump.

Dabiri-Erewa tace a ‘yan makonnin nan dai ofishinta ya sami rahotannin hana wasu ‘yan Najeriya da ke da sahihan takardun izinin shiga Amurka shiga cikin ‘kasar, inda aka tisa keyarsu zuwa gida Najeriya, ba tare da am basu wani kwakwkwaran dalili ba.

Tun lokacin da ya dare karagar mulki shugaba Donald Trump, ya fara cika alkawuran kamfe da ya yi musamman abin da ya shafi shigar baki Amurka, da tuni wata kotun kasar ta ja masa burki.

Najeriya da Amurka dai na ‘dasawa kafin da kuma bayan hawan shugaba Trump, abin jira a gani dai shine yadda huldar diplomasiyyar kasashen biyu zai sa gaba, biyo bayan da abin da a halin yanzu Najeriyar ke ganin tamkar cin fuska ne.

Your browser doesn’t support HTML5

NAJERIYA: Bulaguro Zuwa Amurka Bai Zama Wajibi Ba - 1'09"