Najeriya Ba Zata Kara Kashe Kudi Ba Don Nemawa Jami’anta Magani A Kasar Waje

Kwararren likita yana bincike kan kwayar cutar Malaeriya a wani asibitin kasar Kenya a watan Nuwambar 2010.

Duk da yake kowanne dan kasa na da ‘yancin fita domin neman waraka daga cutar dake damunsa, babban abin takaici inji shugaban Najeriya Mohammadu Buhari, a ta bakin ministan lafiya, shine yadda yan kasar ke yin tururuwa a kasashen waje domin neman maganin rashin lafiya.

Duk kuwa da cewa akasarin cutar ana iya maganinsu a Najeriya, ministan lafiya yace kiyasi ya nuna cewa Najeriya tana asarar kudade da adadinsu yakai Dalar Amurka Dubu 100 a kowacce shekara, da yan kasar ke kashewa a yawon neman lafiya a wasu kasashe. Wanda wannan adadin ya zarta kasafin kudin wasu jihohi a Najeriya.

Hakane yasa shugaban yace gwamnati ba zata kara kashe kudin jama’a ba domin nemawa jami’anta magani a kasashen waje, musamman cututtukan da za a iya maganinsu a cikin gida.

To sai dai duk da yake gwamnatin ta Najeriya tayi alkawarin kyautata tsarin na kiwon lafiya domin aiwatar da wannan kudiri na ta. Mahalarta taron na ganin lamarin da wuya duk da yake zai yi tasirin gaske wajen bunkasa sha’anin kiwon lafiya a kasar.

Wannan na zuwane a taron kungiyar likitoci ta Najeriya a Sokoto, inda kuma aka zabi sabbin shugabannin kungiyar na kasa, kuma taron yazo ne dai dai lokacin da gwamnati ke kokarin dinke wata tankiya tsakaninta da kungiyar likitocin, wadda ke barazanar shiga yajin aiki muddin gwamnati bata biya wasu bukatunta ba.

Domin karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya Ba Zata Kara Kashe Kudi Ba Don Nemawa Jami’anta Magani A Kasar Waje - 3'00"