A lokacin da yake zantawa da wakilin Muryar Amurka, Hasssan Maina Kaina, Aliko yace akwai boyayyun hanyoyi sama da Dubu 2, wanda ta hanyoyinne ‘yan ta’adda ke shigar da makamansu cikin Najeriya.
Muryar Amurka ta tuntubi kakakin rundunar hadin gwiwar kasashen dake yaki da yan Boko Haram a yankin tafkin Chadi, kanar Mohammed Dole, wanda yace su dai basu ga wadannan makaman ba kuma rundunoninsu dake kan bakin iyaka basu yi bayanin kama wasu makamai ba.
Da yake bayar da shawara kan yadda za a iya shawo kan lamarin, Aliko El-Rashid, yace yakamata gwamnatin tarayya ta hada kan shugabannin gargajiya da mutanen dake garuruwan dake bakin iyaka, a samu masu aikin sa kai da zasu ke kula da duk abinda ke shigowa ta kowacce kusurwa, wanda hakan zai taimakawa sojojin hadin gwiwa a kokarin da suke na samar da zaman lafiya a kasashen.
Domin karin bayani.