Rahotanni daga Najeriya na cewa an samu wata hatsaniya a taron jam’iyyar APC na jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin kasar, lamarin da ya kai ga wani dan sanda ya harbi tsohon dan majalisa, Opeyemi Bamidele, kamar yadda kusan daukacin jaridun kasar suka ruwaito.
Baya ga shi Bamidele, jaridun sun ruwaito cewa wasu mutane uku sun samu raunuka a taron wanda aka shirya shi a jiya Juma’a domin tarbar Dr. Kayode Fayemi a yankin Ikere-Ekiti na jihar ta Ekiti.
Dr. Fayemi shi ne dan takarar gwamna a karkashin jami’yyar ta APC a jihar ta Ekiti a zaben da za a yi kwanan nan a cewar jaridar Vanguard.
Bayanai sun yi nuni da cewa, dan sandan ya bude wuta ne a daidai lokacin da Dr. Fayemi zai fice daga filin da aka yi taron domin zagaya gari, lamarin da ya sa matasa da dama suka yi tururuwa, ya kuma harzuka dan sandan ya bude wuta.
Shafin yanar gizon Jaridar The Nation, ya ruwaito cewa, an harbi Bamidele ne a hannu, wanda tsohon mamba ne a zangon majalisar wakilai ta bakwai.
Rahotanni sun ce an garzaya da shi zuwa wani asibitin da ba a bayyana sunansa ba.
Sannan hukumomin ba su bayyana ko an samu asarar rayuka a wannan hargitsi ba.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, ba a bayyana sunan dan sandan da ya yi harbin ba, kuma ba a bayyana dalilinsa na bude wuta ba.
Amma an ce an karbe bindigar hannunsa bayan da matasa suka nakada masa duka, inda da kyar aka kwace shi inji jaridar ta The Nation.