Na Daina Yi wa Mata Kwalliya – Mansur Make Up

Mansur Make Up, mai yi wa jarumai kwalliya a masana'antar Kannywood (Hoto: Instagram/Mansur Make Up)

“Yanzu kan na yi nadama, in Allah ya yarda kuma ba zan sake yi wa wata mace a duniya kwalliya ba.” In ji Mansur Make Up.

Fitaccen mai yi wa jarumai kwalliya a masana’antar Kannywood da ke arewacin Najeriya, Mansur Make Up, ya ce ya daina yi wa mata kwalliya bayan da ya saurari wa’azin da malamai suke yi kan hadarin da ke tattare da yin hakan.

Mansur na daya daga cikin fitattun masu yi wa jarumai kwalliya a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood ciki har da mata.

“Bai kamata a ce namiji na yi wa mace kwalliya ba, ko kuma mace ta zo gabanku tana saka kaya ko ‘acting’, bai kamata ba, ba a abin da zan iya ci gaba ba ne gaskiya.

“Yanzu kan na yi nadama, in Allah ya yarda kuma ba zan sake yi wa wata mace a duniya kwalliya ba.” In ji Mansur Make Up a wata hira da ya yi da Freedom Radio da aka wallafa a shafin Facebook.

A cewar Mansur, farin cikinsa shi ne, babu wanda ya koyawa wannan sana’a a lokacin da yake yi.

A ‘yan kwanakin baya, hukumar Hisba a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Njeriya ta yi taruka da masu ruwa da tsaki a masana’antar ta Kannywood, inda ta ja hankaulansu kan wasu daga cikin ayyukansu da ka iya lalata tarbiyya.