Mutuwar Freddie Gray Kisan Kai Ne

Dan zanga-zanga

Babbar mai gabatar da kara a Baltimore da ke gabashin Amurka ta tuhumi ‘yan sanda guda 6 da laifi game da kama Freddie Gray inda tace mai binciken lafiya na jihar ya tabbatar da mutuwar Freddie a hannun ‘yan sandan da cewa kisan kai ne.

Babbar lauyar gwamnatin Jihar Maryland dake Baltimore, Marilyn Mosby ta fada a ranar juma’a cewa Freddie Gray ya yi fama da matsanancin ciwon wuya a lokacin da ake dauke dashi a motar ‘yan sanda ranar 12 ga watan Afrilu.

Tace ba a saka masa madaurin kujarar mota ba sannan ‘yan sandan basu ba shi ko kuma neman agajin asibiti ba duk da Gray ya nemi taimakon hakan. Sannan tace kama shin da suka yi ma ya sabawa doka.

‘Yan sandan dai an bada belinsu a ranar juma’ar da ta gabata bisa zarginsu da laifin kisan kai da rashin nuna halayya mai kyau da tsare mutum ba bisa doka ba.

Sai dai kuma a halin da ake ciki ‘yan sanda sun kama wasu masu zanga-zanga da suka ci gaba da zama a wajen da aka yi zanga-zangar ta ranar juma’a bayan ansa dokar hana fita a garin.

Masu kallon al’amura sun ce ‘yan sanda sun yi karfa-karfa ga masu boren fiye da yadda suka yi a bayan kafin tuhumar. Jama’a da dama sun taru suna murnar tuhumar da aka yiwa ‘yan sandan.