Fiyeda mutane dubu daya ne jiya Laraba suka yi maci kan titunan birnin Baltimore dake jihar Maryland anan Amurka, a cikin yanayi da kwamishinan 'Yansanda na birnin ya kira "zanga zangar lumana mai tsanani". Masu maci suna neman ganin ana yiwa duka Amurkawa adalci.
Gungun mutanen sunyi maci daga babbar tashar jiragen kasa zuwa helkwatar mulki na birnin sannan suka sake komawa inda suka faro zanga zangar. 'Yansanda sun ce suna fatan dokacin jama'a su mutunta dokar hana fita da aka kafa.
An gudanar da wasu macin a biranen Washington DC, da Boston, da New York inda 'Yansanda suka kama wadansu daga cikinsu kan zargin sunyi kokarin su hana zirga zirgar masu sifiri.
Gwamnan jihar Maryland Larry Hogan ya ayyana Baltimore a zaman birnin da aka maido da doka da oda a wunin jiya Laraba, bayan borin da ya biyo bayan jana'izar wani matshi bakar fata wanda ya mutu yayin da yake hanun 'Yansanda a birnin.
Mutane sun koma harkokinsu na yau da kullum. Motocin safa safa da jiragen kasa suna cike makil da bil'adama a wunin na jiya Laraba. Tawagar makadan zamani na birnin da ake kira Baltimore Symphony Orchestra sun nishadartadda jama'a.
Amma kungiyar kwallon gora na birnin da ake kira Orioles da takwaran karawarsu Chicago White Sox sun kara ba tareda 'yan kallo ba, saboda 'Yansanda sun ce basu da karfin samarda tsaro a filin wasan.
Ranar Litinin masu zanga zanga sun kona shaguna masu yawa da motoci kuma suka wawushe wata babbar kasuwar zamani. Al'amarin ya biyo bayan jana'izar Freddie Gray matashi bakar fata dan shekaru 25 da haifuwa wanda ya mutu a hanun 'Yansanda.