Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zanga-Zangar Garin Baltimore Ta Lafa


Dan Zanga Zanga
Dan Zanga Zanga

Kwamishinan ‘yan sanda Baltimore dake gabashin Amurka, yace hankula sun kwanta yayin da hukumomi suka sa dokar hana fita bayan rikicin da ya barke a ranar litinin, sanadiyar mutuwar wani bakar fata da ya rasu a hanun ‘yan sanda.

‘Yan sanda sun tunkari wasu masu zanga zanga da suka bijirewa dokar hana fitar, wacce ta fara aiki a jiya talata da karfe goman dare. Masu zanga zangar sun taru ne a wata mahada da ke yammacin Baltimore, inda zanga zangar ta ranar litinin ta fi muni.

Bayanai sun ce a lokacin da ‘yan sanda suka nemi masu zanga zangar su watse, sai suka fara jifan ‘yan sandan da duwatsu da kwalabe suna kuma yi musu ihu. Wanda sai bayan kusan sa’a guda sannan suka watse daga wuraren da suke.

Hotunan bidiyon gidajen talbijin sun nuna jami’an tsaro na musamman da ke kwantar da tarzoma, suna sintiri akan tituna a cikin motocin sojoji bayan da aka fara dokar. Sai dai a wani bangaren an ga mazaunan birnin na Baltimore sun fito a jiya talata suna share tituna yayin da wasu ke nuna alhinin kone-kone da wawure kayayyakin shagunan da aka yi.

Magajiyar garin, Stephanie Rawlings Blake, ta kwashe mafi yawan lokutan a jiya talata tana ziyartar wuraren da zanga zangar ta shafa.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG