Mafi yawancin masu zanga-zangar dai matasa ne, wadanda suka faffasa shaguna suka kwashe kayayyaki, a daren jiya kuma suka kona wani babban shago da wasu manyan gine-gine guda biyu dake tsakiyar birnin. ‘yan sanda sama da 12 sun jikkata yayinda suka yi kokarin kwantar da tarzomar.
A yau Talata gwamna Larry Hogan na jihar Maryland dake gabashin Amurka, ya kafa dokar hana fita daga karfe 10 na dare zuwa karfe 5 na safiya, bayan haka kuma an tura dogarawan wanzar da zaman lafiya na kasa a garin na Baltimore don kwantar da tarzomar.
A halin da ake ciki dai yanzu, an kame mutane sama da talatin kuma kurar ta dan natsa duk da cewa jama’a sun yi cincirindo a wata unguwa da ake kira North Avenue a birnin na Baltimore, inda aka kona wani baban shago jiya.
Ranar 19 ga watan Afirilun nan ne wani matashi mai suna Freddie Gray, dan shekaru 25 da haihuwa ya mutu yayinda yake tsare a hannun ‘yan sanda. Abinda ya haddasa zanga-zangar lumana wadda ta rikide ta koma tarzoma.