Mutumin Da Ya Kai Hari Birnin New York Ya Fara Samun Sauki A Asibiti

Ahmad Khan Rahami

Mutumin da ake kyautata zato shine ya tada da bam a daren Asabar a birnin New York da ya ranauta mutane 29, ya fara samun sauki a asibiti daga raunin harsashi bayan harbi da yan sanda suka yi mashi.

Masu shigar da kara sun tuhumi dan shekaru 28 da haifuwar mai suna Ahmad Khan Rahami da aikata laifuka biyar da suka hada da yunkurin kisa, sakamakon musayar wutar da tayi sanadin raunata ‘yan sanda biyu.

An kama Rahami ne a unguwar Linden a jihar New Jersey kusa da Manhattan, sa’o’I kadan bayanda yan sandan New York suka yayata hoton Rahami a kafofin labarai, inda suka sanar suna nemansa domin yi masa tambayoyi.

Wani mai mashaya a unguwar Linden ne ya kira yan sanda da safiyar jiya Litini domin basu rahoton cewa, wani mutum na kwance yana barci a kofar mashayarsa. Yan sanda sun tantance mutumin Rahami ne, wanda ya bude wuta kan yan sandan ya raunata biyu kafin a harbeshi.


Babu wanda yaji rauni mai tsanani dake barazana ga rayuwarshi.Kawo yanzu dai, ba a san dalilin da ya kaishi ga kai harin boma boman ba.