Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutumin Da Ya Soke Mutane 9 Da Wuka A Minnesota Dan Somalia Ne


Minnesota
Minnesota

An gano cewa mutumin da ya soke mutane tara a wata kasuwar zamani ta jihar Minnesota dake arewacin kasar Amurka wani Ba’amurke ne amma dan asalin a kasar Somalia.

Shugaban al’umman Somalia na jihar ya shaidawa sashen Somalia na Muryar Amurka cewa wanda ake tuhumarsa da wannan aik-aikar da yan sanda suka harbe har lahira sunansa Dahir Adan.

Shugaban al’umman Somaliar Abdul Kulane yace mutanensu sun san Adan ne a matsayin wanda ke aiki tsaro na dan lokaci kuma mutum ne mai fasaha kuma amintacce.

Kulane ya kara da cewa ya kasa gane dalilin da ya iza shi yin wannan abu ko kuma dai ba fahimci al’amarin ba.

Ma’aiakatar liken asirin Amurka tana binciken batun sukar a matsayin abinda ke iya zama ta’addanci.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG