An kashe sojojin India 17 wasu kusan 20 kuma sun jikkata a wani mummunan hari da mayakan sakai suka kai a fiyeda shekaru 20, a farmakin da suka auna kan wani sansanin sojojin India a Kshmir, kusa da kan iyakar kasar da Pakistan.
Jami'ai suka ce wasu mayakan sakai cikin damara mai dauke da bindigogi da gurneti ne suka yi dirar mikiya kan sansanin sojojin da yake wani wuri da ake kira Uri wanda yake yammacin Srinagar babban fadar Kashmir na India da sanyin safiyar yau Lahadi.
Wata sararnawar sojin kasar tace an kashe maharan su hudu duka.
A jerin bayanai a shafinsa na Tweeter,PM India Narenda Modi yayi Allah wadai cikin kakkausar harshe kan harin da aya kira "na ta'addanci na ragaye." Yace "ina tabbatarwa kasan nan cewa, wadanda suke da hanu a harin zasu fuskanci shari'a."
Harin a ranar Lahadi nan,zai kara zaman dar-dar tsakanin makwabtan kasashen biyu India da Pakistan masu karfin Nukiliya, wanda dukakknasu biyu, suke ikirari kan yankin na Kashmir baki daya.
Ahalinda ake ciki kuma,'Yansanda a Pakistan sukace wasu 'yan binidga akan Babur sun kash sojojin kasar uku, a bayan garin Peshwar, helkwatar lardin Pakhtunkwa. Sojojin suna cikin wata mota ce lokcinda maharan su far musu.