Bayan shekaru biyar yana shakkun inda aka haifi shugaba Barack Obama, dan takarar shugabancin Amurka Donald Trump, yanzu ya ce "an haifi Obaman a Amurka, iyakar magana."
A shekara ta 2011 ne dan takarar na jam'iyyar Republican ya zama jagoran wata hadaka dake ikirarin ba tareda wata shaida ba, cewa an haifi Mr. Obama a ketare.Tun sannan Trump yaki ya fito kai tsaye yayi magana kan abund a yake ji gameda batun , kamin jiya jumma'a ya kawo karshen surutan.
A wani gangamin siyasa da yayi jiya anan birnin Washington, Trump ya zargi abokiyar takararsa Hillary Clinton a zaman wacce ta fara yada wannan magana lokacin da tayi takara da Obama a shekara ta 2008, amma binciken da kafofin yada labarai da yawa suka yi, ba su ga wata shaida da zata gaskanta wannan zargi ba.
Bayan wannan sanarwar ce ake sa ran Mr Trump zai jagoranci 'yan jarida zagayawa cikin wani sabon O'tel da ya gina anan Washington,amma kwamitin yakin neman zaben Mr. Trump, ya hana wasu 'yan jarida shiga, lamarin da ya janyo gardama, 'yan jaridar baki daya suka janye daga ziyara cikin sabon O'tel din.
Yayinda take magana a wani taron mata bakar fata anan Washington DC, wuni na biyu da komawa fagen yakin neman zabe, bayan rashin lafiyar da ta yi, Mrs. Clinton tayi watsi da wannan sabon yunkurin na Trump tana mai cewa "shekaru biyar ya jagoranci yunkurin mai da bakar fata na farko da ya jagoranci Amurka, a zaman wadda ba dan kasa ba. An kafa harshashin yakin neman zabensa baki daya kan karai-rayi."