Mutumin Da Ya Kafe Yin Kisa A Facebook Ya Kashe Kansa

Steve Stephens

Steve Stephens

Jiya Talata aka kawo karshen farautar wani mutum, wadda aka yi a fadin Amurka, bayan da mutumin, wanda aka zarga da saka bidiyon kisa da ya yi a kafar Facebook ya harbe kansa, bayan farararsa da 'yan sanda su ka yi na wani dan gajeren lokaci, a cewar hukumomi.

An zargi Steve Stephens da bindige wani tsoho har lahira a Cleveland, da ke Ohio, a ranar Lahadi ta Easter, kafin ya saka bidiyon kisan a kafar Facebook, sanna ya shiga gudun 'yansanda.

Hukumar 'yansanda a Pennsylvania ta fadi a kafar Twitter cewa 'yansanda sun hango Stephens a Karamar Hukumar Erie jiya Talata.

"Bayan an farare shi na wani dan lokaci, sai Stephens ya harbe kansa," a cewar 'yansanda.