Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Papa Roma Mai Ritaya Ya Cika Shekaru 90 A Duniya


Tsohon Papa Roman mai ritaya Pope Benedict XVI ya yi bukin cika shekaru casa’in a duniya a wani kwarya kwaryar liyafar iyalai da abokan arziki.

Wasu hotuna da aka nuna a Telabijin fadar Vatican ya nuna Benedict na zaune da bakinsa a wajen gidansa a fadar Vatican inda yake rayuwarsa tun bayan da ya yi murabus a matsayin Papa Roman a sheakarar 2013.


Wansa Monsignor Georg Ratzinger da yake a Jamus ya halarci taron bukin ranar haifuwar tare da wasu mahalarta.


Papa Roma Benedict ya cika shekaru casa’in ne a shekaranjiya Lahadi wanda yazo daidai da ranar bukin Faska na wannan shekara, don haka ya yi bukin ranar haifuwarsa ne a jiya Litini.


Aranar Alhamis magajin Benedict Papa Roman mai ci yanzu Francis ya kai masa ziyara a gidansa don yi masa barkar ranar haihuwarsa.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG