Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Afirka Ta Kudu Za Su Nuna Rashin Amincewarsu Da Shugaba Zuma


Matakan raba raini da al’ummar kasar Afrika ta Kudu suka shafe makonni suna neman ayi mai yiwuwa bazai faru nan da nan ba.

Biyo bayan daga lokacin kada kuri’ar rashin gamsuwa da aiki shugaban kasar da farin jininsa ke dushewa, bayan dage yanke hukuncin da wata babbar kotun kasar ta yi, daga yau Talata zuwa wani lokaci nan gaba.

Dage wannan shari’a wani sabon babi ne a wannan dambarwar siyasa da ke faruwa a Afrika ta Kudu.

Babbar jam’iyar adawa ta Democratic Alliance (DA) itace ta bukaci yan kasar su nuna rashin amincewarsu ga shugaban wanda aka shirya yi a yau 18 ga watan Afrilu a matakin martani kan korar wani ministan kudi da ake matukar mutuntawa da bai kwantawa al’ummar kasar a rai ba, a wani garanbawul da shugaba Jacob Zuma ya yi.

Wannan cece-kucen siyasar ya sa cibiyoyi masu sa ido a kan al’amuran siyasa sun rage matsayin kasar sakamakon wannan batu da ke yin mummunar tasiri ga tattalin arzikin kasar.

Bayan babbar jami’iyar adawa ta DA ta kai kara kotu, wata karamar jami’iyar adawa ta United Democratic Movement ta nemi a kada wannan kuri’a a asirce wanda galibin jama’a ke ganin shine ya ingiza yan jami’iyar shugaba Zuma ta African National Congress ANC su caccaki shugaban nasu.

Wannan ne ya kai ga bukatar kada kuri’ar rashin amincewa ga matakin shugaba a kotun kasar a asirce.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG