Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Theresa May Ta Nemi a Gudanar Da Zabe Da Wuri


Firai Ministar Birtaniya, Theresa May, ta yi kiran a gudanar da zabe da wuri a ranar 8 ga watan Yuni. A yau Talata May ta yi wannan kira, wanda ta ce shi ne hanyar da za a samu daidaito.

Wannan a cewar rahotanni wani mataki ne na samun damar ta saukaka wa kanta shirye-shiryen ficewar kasar daga kungiyar Tarayyar Turai.

Tun bayan makwannin du suka wuce a lokacin da aka amince da amfani da sashen nan na 50, wanda zai bai wa kasar damar fara shirin fice wa daga kungiyar ta Tarayyar Turai, masu adawa da yunkurin ficewar kasar daga tarayyar suke ta zanga zanga.

Za dai a iya kwashe har tsawon shekaru biyu an kici-kicin ficewar kasar daga kungiyar.

Masu fashin bakin siyasa sun ce wannan kira na a gudanar da zabe cikin sauri da May ta yi, wani mataki ne a kokarin ta na karfafa hadin kan masu ra’ayin mazan jiya domin a samu saukin wuce wannan ce-ce-ku-cen da ake yi.

Bisa tsarin doka, a shekarar 2020 ya kamata a gudanar da zabe a kasar ta Birtaniya.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG