Allah ya yiwa mutumin da ya kafa kamfanin Apple kuma tsohon shugaban kamfanin Steve Jobs rasywa. Jobs wanda ya rasu yana da shekaru 56 a duniya, yayi fama da sankarar madata tun shekara ta dubu biyu da uku, aka kuma sake mashi hanta cikin shekara ta dubu biyu da tara.
Kamfanin fasahar ya buga sanarwa a shafinshi na internet jiya da yamma cewa, ya yi rashin mutum dake cike da baiwa da hangen nesa, kuma duniya tayi rashin mutum dake da basira mai ban mamaki. Sanarwar ta kara da cewa, manufarshi zata ci gaba da kasancewa fandeshan na kamfanin Apple.
Shugaban Amurka Barack Obama ya bayyana ta’aziyarshi a wata sanarwa da ya rubuta, da cewa, Jobs yana cikin shahararrun Amurkawa wadanda suka kirkiro wani sabon abu. Mr. Obama yace Jobs ya sauya aikin masana’antu baki daya, ya kuma maida hanyar sadarwar internet, ba abinda kowa zai iya amfani da ita ba kadai, amma wata hanyar koyarwa mai dadin amfani. Wanda ya kuma cimma abinda shugaba Obama ya bayyana a matsayin nasarar da ba safai ake samun wanda zai iya cimma ba, yayinda ya kuma sauya yadda muke kallon duniya.
Jobs ya yi murabus daga shugabancin kamfanin a cikin watan Agusta. An haifi Jobs wanda bai kamala jami’a ba, ranar 24 ga watan Fabrairu shekara ta dubu da dari tara da hamsin da biyar, ya kuma girma a bangaren California wanda daga baya ake kira Silicon Valley, cibiyar kamfanonin fasahar Amurka.
Jobs ya ajiye aikin da yake yi da wani mai silman bidiyo a shekara ta dubu da dari tara da saba’in da hudu ya tafi kasar Indiya domin neman karuwa ta fannin ruhaniya. Bayan dawowarshi, shi da abokinshi Steve Wozniak suka fara aiki a garenjin motar gidansu Jobs, inda suka kera na’urar computer Apple ta farko. Mutanen biyu ne kuma suka kafa kamfanin computer na Apple. Jobs ya rasu kwana daya bayanda kamfanin Apple ya kaddamar da wata sabuwar wayar salulu Iphone wadda ake ba umarni da maganar baki.