Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Miliyoyin mutane suna makokin rasuwar Steve Jobs


Wani matashi yana addu'a bayan ajiye fure domin karrama Steve Jobs.
Wani matashi yana addu'a bayan ajiye fure domin karrama Steve Jobs.

Shagunan kamfanin komfuta na Apple a duk fadin duniya sun zama maziyartar daya daga cikin mutanen da suka kirkiro kamfanin Steve Jobs wanda ya rasu ranar Laraba yana da shekaru 56.

Shagunan kamfanin komfuta na Apple a duk fadin duniya sun zama maziyartar daya daga cikin mutanen da suka kirkiro kamfanin Steve Jobs wanda ya rasu ranar Laraba yana da shekaru 56.

Jama’a sun ajiye furanni da kyandira a shagunan jiya alhamis, yayinda miliyoyin mutane a duk fadin duniya suke makokin mutuwar mutumin da ya zama jagoran kimiyyar kere-kere wanda ya kera na’urori iri-iri da suka sauya salon kade-kade da wake-wake, da wayar salula da kuma masana’antar komfuta.

Labarin mutuwar Jobs ya isa kowanne bangaren duniya har tashar jirgin jigila kimiyya ta kasa da kasa inda kwamanda Mike Fossum ya bayyana shi a matsayin mutum mai hazaka da basira da kuma baiwar kirkire-kirkire.

Babban magatakardar MDD Ban ki-moon ya bayyana Jobs a matsayin mutum wanda jagoranci duniya ta wajen basirarshi fiye da kowa. Shi kuwa mutumin da ya kafa hanyar sadarwa ta Facebook Mark Zuckerberg godewa Jobs ya yi domin nuna cewa, abinda ya kafa zai iya canza duniya.

A nashi bangaren, tsohon shugaban Amurka Bill Clinton ya bayyana cewa, irin sha’awar aikin da Jobs yake da shi, da kuma karfin halin da ya nuna yayin jinyar cutar daji sun zama koyi.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG