Sojojin Ruwan Mexico sun ce an gano gawarwakin mutane 32 a jihar Veracruz da ke gabashin kasar, inda aka watsar da wasu dinbin gawarwaki kan hanya da tsakar rana a watan da ya gabata.
An gano gawarwakin ne jiya Alhamis cikin wasu gidaje 3 da ke wata tashar jirgin ruwa, wadda ta zama tamkar fagen munanan fadace-fadace tsakanin masu safarar muggan kwayoyi.
Hukumomi na kyautata zaton masifaffiyar kungiyar “Zetas” ta masu safarar muggan kwayoyin nan na da hannu a mutuwar mutane 35 da aka gano gawarwakinsu a watan jiya an watsar bisa wata babbar hanyar cikin gari a Veracruz.
Shugaba Felipe Calderon ya girke ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a Veracruz.
An hallaka sama da 40,000 a Mexico tun bayan da Shugaba Calderon ya kaddamar da shirin yaki da safarar muggan kwayoyi a 2006.