Indiya ta kaddamar da abun da ta kira kwamfuta mafi araha a duniya, da nufin baiwa talakawan kasar damar mallakar na’urar.
Kwamfutar mai suna “Aakash” wato samaniya, da yaren Hindi, za a saida ta ga dalibai akan dola 35 da tallafin gwamnati.
Jami’an gwamnatin kasar Indiya da kamfanin DataWind Limited, wanda ya kera kwamfutar, sun rarraba ta a yau Laraba ga daruruwan dalibai a birnin New Delhi, kamfanin zai gwada ingancin kwamfuta dubu dari tukuna kafin ya, sa su a kasuwa. Kwamfutar za ta bada damar yin rubuce-rubuce, da shiga intanet, da yin magana ta bidiyo da wasu mutane, kuma ta na da layuka biyu na hada ta da kemara, da kuma wata na’urar sauti.
Babban darektan kamfanin DataWind Limited Suneet Singh Tuli ya yi kira a yau Laraba cewa wasu kamfanoni ma su kirkiro na su samfurin kwamfuta ta yadda farashin kwamfuta zai yi kasa warwas a kasar har ma ya kai ga dola 10.
Ministan habaka ci gaban rayuwar jama’a na kasar Indiya Kapil Sibal ya bayyana cewa wannan kwafuta,kyauta ce ruwan Allah ga illahirin yaran kasar kuma wata hanya ce wadda za ta taimakawa wasu da dama su fita daga kangin talauci.
Kasar Indiya dai ta yi suna wajen kirkiro sabbin kayayyaki masu rahusa da kowa ke iya saye, akwai ma wata ‘yar kankanuwar motar da ake sayarwa akan dola dubu biyu.