Justin Mohn, mai shekaru 32, wanda ake tuhuma da laifin kisan kai da kuma cin zarafin gawa, yana dauke da makamai yayin da ya tsallake shingen tsaro a wata cibiyar tsaro ta kasa mai nisan mil 100 (kilomita 160) a lokacin da aka kama shi da yammacin Talata, sa'o'i bayan kisan a cewar mai magana da yawun rundunar tsaron.
An sami mahaifin na sa, mai suna Michael F. Mohn, da kan shi a yanke a bayan gidan na su da ke Levittown inda shi ma dansa ke zaune.
A cikin wani bidiyon YouTube, wanda ya wuce mintuna 14, ya nuna Justin Mohn yana rike da kan sama tare da bayyana sunan mahaifinsa. ‘Yan sandan sun ce ga dukkan alamu yana karanta abinda yake fada ne, yayin da yake bayyana goyon bayan cin zarafin jami’an gwamnati tare da kiran mahaifinsa mai cin amanar kasars
Michael Mohn ma'aikacin gwamnatin tarayya ne, kuma injiniyan sashen yanayi a ofishin rundunar sojojin Amurka da ke aiki a gundumar Philadelphia, in ji kakakin hukumar Steve Rochette. Rochette ya ƙi ƙarin bayani.
‘Yan sanda sun ce matar Michael Mohn, Denice Mohn, ta isa gida ne ta gano gawar da misalin karfe 7 na dare a ranar Talata. Jami’an sun gano gawar, adduna da safar hannu na roba mai jini a jike, a cewar sanarwar ‘yan sanda.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, kamfanin YouTube ya ce an cire bidiyon, wanda aka loda kuma ba a yada shi ba, an cire shi ne saboda karya manufofinta na tashin hankali, an kuma rufe tashar Justin Mohn.
Mohn, wanda shi ma aka kama shi da laifin mallakar makamai, an gurfanar da shi a ranar Larabar da ta gabata kuma an tsare shi ba tare da beli ba, yayinda aka tsaida ranar 8 ga watan Fabrairu a matsayin ranr da za a saurari karar..