Hukumar hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA a Najeriya, ta ce akwai akalla mutum sama da miliyan 15 da ke ta’ammali da miyagun kwayoyi a kasar.
Shugaban hukumar, Janar Buba Marwa mai ritaya, ya ce lamarin na taka muhimmiyar rawa wajen wanzuwar matsalar garkuwa da mutane, da ayyukan ‘yan bindiga da kuma rikicin Boko Haram.
“Za su kai miliyan 15, kuma wannan lissafi ne sosai na United Nations (Majalisar Dinkin Duniya,) ba kawai mun fada ba ne, ka ga ba karamin lamba (adadi) ba ne wannan.”
“Ya zama dole wannan yaki ya soma daga iyaye, wato tarbiya. Iyaye da kansu dole su lura ko akwai wani canji tattare da yaransu. Shin yara suna sa turare masu nauyi don su boye warin wani abu, ko suna tafiya daidai ko suna tafiya suna tangadi?”Janar Marwa ya ce a hirarsu da wakilin Muryar Amurka Alhassan Bala.
Ku Duba Wannan Ma Marwa Na So A Rika Yi wa Daliban Jami’a Gwajin Amfani Da Miyagun KwayoyiShugaban na NDLEA ya kara da cewa, hukumar ta na shirin gudanar da gwajin kwaya ga ‘yan takarar a zabukan 2023 a wani bangare na yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi.
“Zan soma kewaya jam’iyyun siyasa, gwamnatin Kano sun riga sun soma irin wannan. Idan za ka nemi takara dole sai an tabbata ba ka shan wani abu. Idan ba haka ba, da zarar ka hau kan kujera, dan kudin da ka samu na jama’a sai ka ga an sayi hodar iblis da su, kuma kai ba zai zama daidai ba.” In ji Marwa.
Kazalika Marwa ya nuna cewa akwai bukatar jami’o’in kasar su fara yi wa daliban da za su dauka gwajin miyagun kwayoyi.
Saurari cikakkiyar hirar:
Your browser doesn’t support HTML5