Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fasinjan Jirgi Ya Yi Kashin Kullin Hodar Iblis 59 Da Ya Hadiye A Abuja


Irin kullin da aka kama Douglas da shi (Twitter/ NDLEA)
Irin kullin da aka kama Douglas da shi (Twitter/ NDLEA)

Gwaje-gwajen na awo da hukumar ta yi, sun nuna cewa nauyin hodar ta iblis ya kai gram 781.2.

Hukumar da ke yaki da mu'amulla da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA a Najeriya, ta kama wani dan shekara 23 da kullin hodar iblis guda 59.

NDLEA ta kama Okoguale Douglas da kulli-kullin hodar ne, yayin da yake kan hanysarsa ta zuwa kasar Italiya daga Abuja, babban birnin Najeriya.

An kuma tilasta mai ya yi kashin su bayan da aka gano yana dauke da su a ranar Juma’a.

Wani bidiyo da hukumar ta NDLEA ta wallafa a shafinta na Twitter, ya nuna Douglas yana fitar da kunshin hodar ta iblis daga wata leda yana ajiyewa a kan wani teburin da ke gaban wani jami’in hukumar, bayan da ya yi ba-hayar su.

Shugaban NDLEA, Muhammad Buba Marwa (Twitter/ NDLEA)
Shugaban NDLEA, Muhammad Buba Marwa (Twitter/ NDLEA)

Bidiyon ya nuna jami’in NDLEA yana gwada kullin a wata na’ura da ke tantance abin da ke kunshe a ciki, inda daga baya na’urar ta tabbatar da cewa haramtacciyar hodar ce.

Gwaje-gwajen na awo da hukumar ta yi, sun nuna cewa nauyin hodar ta iblis ya kai gram 781.2.

Wata sanarwa da NDLEA ta fitar, ta ce Douglas dan asalin karamar hukumar Esan North-East ne a jihar Edo da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Sanarwar ta kara da cewa Douglas na ikrarin wani mutum ne ya ba shi ya kai masa hodar birnin Milan da ke kasar Italiya, inda aka yi masa alkawarin za a ba shi Euro dubu biyu a matsayin tukwici – kwatankwacin naira dubu 925.

NDLEA ta ce tana ci gaba da bincike domin kokarin gano ko akwai wasu da ke da hannun a yunkurin safarar hodar ta iblis.

Jirgin da Douglasa ya shirya bi, zai tashi ne daga Abuja, ya tsaya a Addis Ababa na kasar Habasha, sannan ya dangana da birnin Milan na kasar Italiya in ji hukumar ta NDLEA.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG