Jami’an gwamnatin kasar Iraqi sun ce wasu fashe-fashe har guda ukku sun girgiza wata kasuwa mai hada-hada a Baghadaza babban birnin kasar, sun halaka mutum 6 a kalla, wasu kuma fiye da 20 sun raunata.
Fashe-fashen boma-boman da suka wakana a kasuwar Shurja ta birnin Baghadaza, sun janyo gobara a wani gefen unguwar ta kasuwanci a yau Lahadi ranar da Musulmi ke Sallar Eid al-Adha ko Sallar Layya.
Yawan tashe-tashen hankula sun ragu a kasar Iraqi, amma har yanzu kusan a kowace rana ana ci gaba da samun munanan hare-haren da ke kisa, hakan kuwa a daidai lokacin da Amurka ke shirin janye duka sojojin ta dubu 33 daga kasar a karshen shekara.