Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mace Macen Bayan Ambaliyar Thailand sun kai 506


Wasu 'yan Thailand na kaurace wa ambaliyar ruwan
Wasu 'yan Thailand na kaurace wa ambaliyar ruwan

Jami’an gwamnatin Thailand sun ce adadin wadanda su ka mutu

Jami’an gwamnatin Thailand sun ce adadin wadanda su ka mutu sanadiyyar ambaliya mafi munin da Thailand ta taba gani cikin shekaru 50 da su ka gabata ya kai mutum 506.

Jami’an na gwamnati su ka ce ambaliyar na barazana ga babban dandalin cinakayyar Bangkok, da sananniyar kasuwar Chatuchak, da kuma hanyoyin jirgi na karkashin kasa, kuma ana shirin saka kwace mutane daga wannan birni mai yawan mutane kimanin miliyan 12.

Kananan hukumomi sun bayar da umurnin a kawashe jama’a a 10 daga cikin gundumomi 50 na birnin Bangkok da kuma kwasar wasu kalilan daga wasu gundumomin akalla 5. To amman mutane da dama sun gwammace tsayawa don kare gidajensu da wuraren sana’o’insu.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG