Wasu 'yan bindiga akan babura dauke da manyan bindigogi sun hallaka Mutane 21 a jihar Naijan Najeriya da tsakiyar ranar Litanin din nan.
Maharan dai, bayan sun kashe wadannan mutanen a kauyukan Kurebe, Sabon Gida, Kauyen Sararai da kuma Rafin Kanya, dukkaninsu a yankin karamar hukumar Shiroro, sun kuma yi awon gaba da wasu mutane kimanin 40.
Lamarin dai ya jefa dubban mazauna yankin cikin wani yanayi na tashin hankali, kamar yadda Malam Galadima Salisu, mazaunin yankin ya bayyana.
Maharan dai sun bar mutane da dama cikin mawuyacin hali, wasu daga ciki kuwa sun samu munanan raunuka.
A tabakin shugaban Kwamitin tsaro na Gwamnatin jihar Naija, Sakataren Gwamnatin jihar Ahmed Ibrahim Matane, ya ce suna da labarin harin, amma basu da tabbacin adadin mutanen da suka mutu.
Gwamnatin jihar na iya kokari don ganin sun samu cikakkun bayanan abubuwan da suka faru, da daukar matakan da suka dace.
A cikin 'yan kwanakin nan jihar Naija ta fuskanci matsaloli na rashin zaman lafiya, an dai sa ran sabbin jami'an tsaro da shugaban kasar ya nada zasu taka muhimmiyar rawa.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari a cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5
Karin bayani akan: Ahmed Ibrahim Matane, jihar Naija, Boko Haram, Nigeria, da Najeriya.