Mutanen Kauyukan Dake Kewayen Maiduguri Suna Kauracewa

Mutanen da suka yi gudun hijira

Sabili da yawan harin da ake kaiwa kan kayukan dake kewayen Maiduguri babban birnin jihar Borno mazauna kauyukan suna kauracewa suna shiga Maiduguri inda suke gudun hijira.
Yawan harin da 'yan kungiyar Boko Haram ke kaiwa kan kewayen Maiduguri ya sa mutanen kauyukan suna kauracewa suna gudun hijira zuwa birnin na Maiduguri cikin jihar Borno.

Rahotanni na cewa daruruwan mutane daga kananan hukumomin Jere da Kondiga suka yi gudun tsira da rai zuwa birnin Maiduguri sakamakon irin hare-haren da ake kaiwa kan kauyuka dake makwaftaka da Maiduguri. Idan ba'a manta ba makon da ya wuce ne wasu 'yan bindiga suka kai hari a wani kauyen da ake kira Alau inda suka hallaka mutane 19 da kuma raunata wasu da dama. A harin dimbin gidaje maharan suka bankawa wuta.

Harin baya bayan nan ya sa kauyukan dake kusa da Alau suka fara gudun hijira zuwa cikin Maiduguri domin tsira da rayukansu.Mutanen da suka hada da mata da kananan yara sun kwashe wajen kwanaki hudu a filin Allah. Wani Ciroma Gwani ya ce tsoro ne ya kawosu.Ya ce babu kowa a kauyukan domin duk sun gudu. Ya ce kakanninsu da iyayensu basu san idan suke ba. Yanzu a jeji suke kwana.

Mutanen dai sun ce lamarin da ya faru a Alau ya tada masu hankali domin babu tabbas ba za'a kawo ma kauyukansu hari ba.Wata ma ta ce an konesu da wuta. Da kyar suka gudu da rayukansu. Abinci da ruwa sun yi masu wuya.

Amma gwamnatin jihar Borno ta kai ziyara a wani wurin da 'yan gudun hijirar suka taru. Ta kai masu gudummawa. Har wa yau gwamnatin ta yi alkawarin kwashesu zuwa wata makarantar firamare inda ta samar masu da kayan agaji kamar yadda jagoran tawagar gwamnati Barrist Kaka Shehu kwamishanan shari'a na jihar ya sanar. Ya ce mutanen sun fito daga kauyuka 21 dalili kenan da gwamnan jihar ya bada umurni a samar masu kayan masarufi da kayan shimfida da na furuwa da buhun shinkafa 200 da birabisko 100 da garwar man gyada 100 da tabarmi 600 da magi katon 100.

Gwamnati ta bamutanen hakuri kuma ta nada kwamitin da zai tabbatar an mayar dasu gidajensu.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Mutanen Kauyukan Dake Kewayen Maiduguri Suna Kauracewa - 3:28