Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 19 a Borno


'Yan bindigar da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne sun kuma kona gidaje, suka kwace motoci a wannan gari mai tazarar kilomita 7 daga Maiduguri.

Wasu 'yan bindigar da ake kyauata zaton cewa 'ya'yan kungiyar na ta Boko Haram ce sun kashe mutane akalla 19, suka raunata wasu da dama a wani harin da suka kai cikin daren da ya shige a kan garin Alau, mai tazarar kilomita 7 daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno.

Mutane kimanin 100 sun gudu sun bar gidajensu daga wannan gari dake yankin karamar hukumar Jere, a bayan da 'yan bindigar suka kona gidajen nasu.

Mutanen garin suka ce 'yan bindigar sun isa can cikin motocin Akori-Kura guda biyu da babura kamar 9, daga bisani kuma wasu karin motoci 4 dauke da 'yan bindiga suka isa garin.

Isarsu ke da wuya sai suka fara bude wuta a kan jama'a, wadanda suka watse, wasu suka shiga daji.

Hukumomin tsaro a Jihar Borno sun ce su na bin diddigin wannan labarin.

Ga rahoton Haruna Dauda daga Maiduguri.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG