Mutanen Ibi Sun Koka da Dokar ta Baci

Yanzu haka al-ummar yankin na cikin wani hali, sakamakon dokar hana fita waje na ba dare ba rana, da aka kafa yau kusan kwanaki hudu.
Mallam Sahalu Sale mazaunin garin Ibbi ne, yace “walLahi muna cikin matsala ne, kuma an takura mu. Jama’a ba ruwan da za’a sha, ga yunwa, anki barinmu. Ana cikin wahala fa. Abunda muke so, gwamnati ta sassauta wannan dokar ta bacin, tunda akwai jami’an tsaro a gari.

Suma matafiya da kan bi garin Ibbin domin zuwa manyan biranen Najeriya suma wannan doka ta shafe su. “Mara lafiya da aka kawo, shima ya mutu, saboda ba’a samu daman wucewa da shi ba”, a cewar wani matafiyi.

To sai dai kuma gwamnatin jihar Taraban tace tana sane da halin al-ummar yankin ke ciki, kuma kamar yadda sakataren yada labaran mukaddashin gwamnan jihar, Mr. Keffas Sule ke cewa nan bada jimawa ba, za’a sassauta dokar.

Mr. Keffas yace “gwamnati ta sa ido a cikin magannan”.

Your browser doesn’t support HTML5

Mutanen Ibbi na Cikin Wani Hali- 2'54"