Yau kimanin watanni biyu ke nan da hukumomin tsaro suka kafa wannan dokar hana fita da dare, karkashin dokar-ta-bacin da aka ayyana a jihar ta Adamawa da kuma jihohin Borno da Yobe.
Mazauna garin na Mubi, wadanda suka yi ikirarin cewa akasarinsu 'yan kasuwa ne, sun fadawa Muryar Amurka cewa ko a bisa kuskure mutum ya kai karfe 7 na maraice a waje, yana fuskantar cin zarafi daga sojoji wadanda suke wulakanta mutane fiye da kima.
Muryar Amurka ta yi kokarin jin ta bakin kwamandan sojojin dake Mubi, Leftana-kanar Kayode Martin, amma bai amsa wayarsa ba.
A halin da ake ciki dai, sabon kwamandan birged ta 23 ta sojojin Najeriya dake Yola, Birgediya-Janar Rogers Nicolas, ya karbi ragamar wannan birged tare da yin kira ga jama'a da su ci gaba da ba su hadin kai, yana mai cewa an fara ganin amfanin matakan da aka dauka, kuma in jama'a suka kara hakuri, nan ba da jimawa ba za a dage dukkan matakan da suke takura musu.