Amurka ce kan gaba a adadin wadanda suka kamu da cutar a kasashen duniya, inda ta ke da mutun miliyan 17.5, sai India da ke bin ta a baya da adadin sama da mutun miliyan 10, daga nan sai Brazil mai adadin mutun miliyan 7.1.
Likitocin da ke koyon aiki sun nuna rashin jin dadinsu a cibiyar lafiyar Stanford da ke Palo Alto a jihar California ranar jiya Juma’a, saboda su da wasu kwararru da ke kan gaba wajen kula da marasa lafiyar COVID-19, ciki har da jami’an jinya da kwararru a fannin numfashi, ba sa cikin lissafin wadanda aka shirya za a ba riga kafin. Cibiyar lafiyar ta Stanford ta basu hakuri ta kuma yi alkawari zata nemo mafita ba tare da bata lokaci ba.
Kafar yada labaran Turkiyya ta ce mutane 8 sun mutu a wata gobara da ta barke a fannin da ake jinyar masu fama da rashin lafiya mai tsanani a asibiti, inda ake jinyar masu COVID-19.
Kafar yada labaran Anadolu ta ce a yau asabar ne gobarar ta tashi a lokacin da wani bututun iskar Oxygen ya yi bindiga a asibitin koyarwa na Sanko a Gaziantep a kudancin Turkiyya.