Mutane Biyu Sun Mutu A Baban Birnin Kasar Burundi

Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza.

Mutne biyu sun mutu a tarzomar da aka yi cikin dare a Bujumbura baban birnin kasar Burundi. Yau Lahadi shedun gani da ido suka bada wannan rahoto a yayinda zaman tankiya ke kara kamari kafin zaben da za'a yi a kasar.

Akalla mutne biyu ne suka mutu a tarzomar da aka yi cikin dare a Bujumbura baban birnin kasar Burundi. Yau Lahadi shedun gani da ido suka bada wannan rahoto a yayinda zaman tankiya ke kara kamari kafin zaben da za'a yi a kasar.

Jam'iyun masu hamaiya a kasar sunce zasu kauracewa zaben da za'a yi domin nuna rashin amincewarsu ga begen shugaban kasar na yin wa'adi na uku akan ragamar mulki.

Kungiyoyin masu hamaiya sunce zasu kauracewa zaben wakilan Majalisar wakilai da za'a yi gobe Litinin da kuma zaben shugaban kasar da aka shirya yi a ranar sha biyar ga watan Yuli, suna masu fadin cewa zai yi wuya a gudanar da zabe cikin adalci.

Masu cacakar manufar shugaba Pierre Nkunrunziza sunce ya keta ka'idar wa'adin mulki biyu kamar yadda tsarin mulkin kasar ya tanada da kuma ka'idodin yarjeniyoyin da suka kawo karshen yakin basasar kasar.

To amma kuma kotun tsarin mulki kasar tace shugaban ya cancanci sake yin takara, domin Majalisar wakilan kasar ce ta zabe shi ba wadanda suka cancanci yin zabe ba a wa'adin mulkinsa na farko a shekara ta dubu biyu da biyar.

Begen shugaba Nkurunziza na yin takara a karo na uku ta hadasa yunkurin juyin mulki a watan jiya. Sa'anan kuma rikicin da ake yi a kasar ta tilastawa fiye da yan kasar dubu dari arcewa zuwa kasashe makwaptan Burundi.