A jiya Juma’a kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Jeff Rathke, ya ce yanayin da kasar ke ciki ba zai ba da damar a gudanar da zabe mai inganci ba.
Ya kuma ce Amurka ta shiga damuwa matuka, bayan wasu hare-haren gurneti da aka kai, da rikicin da tsagerun ke haifarwa, da tsaurara matakan hana zanga zangar lumana da walwalar ‘yan jarida, duk suna yin hanun riga a kokarin da ake yi na shawo kan rikicin.
A harin gurneti da aka kai a kofar wani banki da ke Bujumbura, wani dan karamin yaro ya samu rauni, sannan wasu mutane biyu sun halaka a wasu hare-hare na daban da aka kai a ‘yan kwanakin nan.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta zargi ‘yan sandan kasar da wuce-gona-da-iri a kokarin da suke yi na tarwatsa masu zanga zanga, wadadan ke adawa da yunkurin da Shugaba Pierre Nkurunziza ke yi na neman tazarce.