A yau Asabar rahotanni daga Jihar Legas a kudu maso yammacin Najeriya sun ce mutane bakwai ne suka rasa rayukansu bayan da wani jirgin ruwa na fasinja ya kife a yankin Ikorodu.
Jami’in hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA, Mr Onimode, ya tabbatarwa wakilin Muryar Amurka a birnin na Eko, Babangida Jibril da aukuwar lamarin.
Kafofin yada labaran kasar sun ruwaito cewa jirgin mai daukan mutane 20 na tafe ne da fasinjoji 17 yana kuma kan hanyarsa ne ta zuwa yankin Badore daga Ijede.
A lokacin hada wannan rahoto, jami’an ba da agajin gaggawa na can suna kokarin lalubo sauran mutane takwasa da ba a gani ba.
Ire-iren wannan hadarin jirgin ruwa, ba sabon abu bane a jihar ta Legas wacce ke kusa da teku kuma mai cunkoson jama’a.
Ababan hawa na sufurin fasinja ya kasance daya daga cikin manyan kalubalen da ke fuskantar jihar a duk lokacin da mutane ke gudanar da harkokinsu na yau da kullum.