Mutane Akalla 150 Suka Mutu A Brazzaville

Wannan hoto da aka cira daga jikin bidiyo tun daga tsallaken kogi a Kinshasa, ya nuna fashewar da ta girgiza Brazzaville, babban birnin Jamhuriyar Kwango, lahadi 4 Maris, 2012.

A bayanda wasu fashe-fashen masu karfin gaske suka tashi a wani wurin tara makamai dake bakin Kogin Kwango

Ma’aikatan diflomasiyya da jami’an gwamnati sun ce mutane akalla 150 sun mutu, cikinsu har da wasu ma’aikata ‘yan kasar China, a lokacin wasu fashe-fashen da suka faru a Brazzaville, babban birnin Jamhuriyar Kwango.

Hukumomi sun ce wasu fashe-fashe masu karfin gaske sun wakana yau lahadi da safe a wani wurin tara makamai dake dab da bakin gabar kogin Kwango.

Wani jami’in jakadancin kasar China a Barzzaville ya fadawa kamfanin dillancin labaran Xinhua cewa akwai ma’aikata ‘yan kasar China su akalla 4 a cikin wadanda suka mutu, yayin da wasu da dama suka ji rauni. An ambaci Duan Jinzhu yana fadin cewa ofishin jakadancin yana kokarin samo karin bayani a game da mace-macen.

Har ya zuwa yanzu ba a san abinda ya haddasa wadannan fashe-fashen ba.

Shaidu sun ce fashe-fashen sun cilla hayaki mai yawa sama, sun kuma ragargaza tagogi a Kinshasa, babban birnin Kwango ta Kinshasa dake tsallaken kogi daga nan.