Mutane 88 Sun Mutu A Wani Harin Bomb A Pakistan 

Harin bomb a wani masallaci a Pakistan 

Wani tashin bam mai matukar karfi, ya tarwatsa wani masallaci mai cinkushe da mutane a Arewa maso yammacin Pakistan a yau dinnan Litini, ya hallaka masu ibada a kalla 59, ya kuma raunata wasu sama da 150. 

WASHINGTON, D. C. - Wani tashin bam mai matukar karfi, ya tarwatsa wani masallaci mai cinkushe da mutane a Arewa maso yammacin Pakistan a yau dinnan Litini, ya hallaka masu ibada a kalla 88, ya kuma raunata wasu sama da 150.

Wannan hari, wanda aka kai da yamma, a yankin tsakiyar Peshawar, hedikwatar lardin Khyber Pakhtunkhwa, an ce aikin wani dan kunar baki wake ne.

Wani babban jami’in tsaro, Mataimakin Kwamishina Shafiullah Khan, ya tabbatar da adadin wadanda abin ya rutsa da su, a wani gidan talabijin na gwamnati, ya na mai fargabar cewa adadin mace-macen ma na iya karuwa.

“Ina nan, inda bam din ya tashi, ina ganin yadda aikin ceto ke gudana, ana ta kawar da baraguzai, kuma yanzun nan ma mu ka zakulo wasu mutane biyu da ransu” a cewar Khan.
-AP