Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Jamiaan Amurka Dana Birtaniya Sun Mutu A Syria Sakamakon Tashin Bomb


Bukin sSa Hannu Kan Yarjejeniya Tsakanin Rundunar Sojojin Nijar Da Ta Jahar Indiana Ta Kasar Amurka,
Bukin sSa Hannu Kan Yarjejeniya Tsakanin Rundunar Sojojin Nijar Da Ta Jahar Indiana Ta Kasar Amurka,

Wasu Maikatan Amurka dana Birtaniya sun mutu sakamakon tashin wani bom a bakin hanya a ranar alhamis a birnin Manbij.

Wasu jamiaan aikin hadin gwiwa dake aiki a kasar Syria, daya Ba-Amurke daya kuma dan kasar Birtaniya sun hadu da ajalin su a sakamakon tashin wani Bomb a bakin hanya a ranar alhamis da daddare, Inji jamiaan kasar Amurka dake kasar, suka ce haka kuma wasu biyar sun samu rauni duka sakamakon wannan tashin bomb din.

Wasu daga cikin jamiaan kasar Amurka da basu yarda a ambaci sunayen su ba sun shaidawa kanfanmin dillacin labrai na Reuters cewa an kai wannan harin ne a birnin Manbij dake arewacin Syria.

Sai dai bayanan farko da ya fito daga sojojin Amurka bai nuna ainihin inda aka kai wannan harin ba, haka kuma basu bayyana sunaye da kasashen wadanda wannan lamari ya rutsa dasu ba, sai dai kawai suka ce maaikatan hadin gwiwa ne.

Mai Magana da yawun sojojin na Amurka Conel Ryan Dillion bai bayyana nan take su wanene keda alhakin kai wannan harin ba amma yace tuni suka tantance binciken su akan wannan harin kuma ba zasu bayyana shi ba a halin yanzu har sai sun kammalla bincike.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG