Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Dan Kunar Bakin Wake Ya Halaka Mutane 15


Harin Kunar Bakin Wake Da Aka Kai Jami'ar Maiduguri
Harin Kunar Bakin Wake Da Aka Kai Jami'ar Maiduguri

Sakamakon harin da wani dan kunar bakin wake yakai a gabashin kasar Afghanistan yayi dalilin mutuwar mutane har 15

Wani dan kunar bakin wake ya tada bomb a wani wurin da ake janaizar tsohon shugaban yankin gabashin Afghanistan dake gundumar Nangarhar.

Wannan wurin da dan kunar bakin waken yakai hari wuri ne da aka jima ana samun yawan samun fito-na-fito da jamian tsaron kasar da kuma kungiyar IS.

Mai Magana da yawun hukumar wannan gundumar Attaullah Khogyani ya fada wa wannan gidan radiyon cewa a kalla mutane 15 ne suka mutu kana wasu 13 suka samu rauni iri daban-daban.

Yawawancin wadanda wannan abin ya rutsa dasu ko fararen hula ne.

Sai dai rahotannin farko sun bayyana cewa mutane 6 ne suka mutu kana 11 suka samu rauni.

Sai dai kawo yanzu ba wani wanfa ya dauki alhakin aikata wannan danyen aikin.

Wannan harin yana zuwa ne kwana daya bayan an kai wa cibiyar al’adun ‘yan Shiite hari a Kabul wanda yayi dalilin mutuwar mutane 41 kana sama da 80 suka samu rauni.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG