Kwalara Ta Hallaka Mutane 583 A Cikin Mutane 23,550 Da Suka Kamu Da Cutar A Najeriya

Cholera

Har yanzu dai cutar kwalera dake sa amai da gudawa na cigaba da addabar mutane a Najeriya.

Kimanin mutane dubu ashirin da uku da dari biyar da hamsin (23,550) ne ake zargin sun kamu da cutar, yayin da mutum dari biyar da tamanin da uku (583) suka mutu sakamakon cutar.

Hakan ya fito ne a rahoton hukumar kare yaduwa da cututtuka ta kasa NCDC da take fitar da bayanai game da cutar ta kwalera.

Rahoton ya bayyana cewa an samu mutuwar mutanen 583 ne a kananan hukumomi 270 na jihohi 32 a fadin kasar, ciki har da babban birnin tarayya Abuja.

Shin me hukumar lafiya matakin farko ke yi game da yaduwar cutar kwalera?

Dr. Abdullahi Bulama Garba shine daraktan tsare-tsare, bincike da kididdiga na hukumar lafiya matakin farko na kasa. Dr. Bulama ya bada shawara da dawo da 'yan duba gari domin tabbatar da tsafta, wanda hakan zai iya rage yaduwar cututtuka tsakanin jama’a.

An samu ambaliyar ruwa a kasar wanda ya kawo gurbacewar muhalli da za a iya cewa shi ne ya haddasa cutar ta kwalera.

Banda cutar kwalera da ake samu, bayan haka kuma akan samu mutane da zazzabin "typhoid".

Saurari rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

CHOLERA-CASES AND DEATHS IN NIG..mp3