Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Kwalara Ta Kashe Fiye Da Mutane 80 a Jihohi 7 Cikin Wata Daya


Wata mata da tana fama da cutar kwalara
Wata mata da tana fama da cutar kwalara

Fiye da mutane 80 ake tsammani sun mutu ta wurin cutar kwalara tun barkewar cutar a shiyoyi daban daban na Najeriya.

Fiye da mutane 80 ake tsammani sun mutu ta wurin cutar kwalara tun barkewar cutar a shiyoyi daban daban na Najeriya. Rohotanni daga sashe daban na kasar sun nuna cutar ta karu cikin watanni biyu da suka shige. Bayan wannan, ta sake barkewa a jihar Oyo, a karamar hukumar Egbeda, da mutane 8 suka mutu aka kuma kwantar da mutane 12 a asibiti.

A jihar Plato, mutane 9 suka mutu daga cutar, wanda ta kama mutane 86 a kauyen Namu, wadanda ke cikin masu gudun hijira fiye da 7,000 wadanda suka gudu zuwa jihar saboda batun kungiyar matsafa ta Ombatse cikin jihar Nasarawa. Cutar kuma ta kama mutane 536 ta kashe 46 a jihar Zamfara kwanannan.

Haka kuma, cutar ta yadu zuwa jihar Sokoto, ta kashe mutane biyar cikin tara da suka kamu da cutar cikin karamar hukumar Tambuwal a watan goma. Wadanda suka kamu sa cutar suna tsakanin shekaru 27 zuwa 30.

Rahotani sun kuma nuna cewa an samu bullat cutar a kudu, musamman jihar Legas, yayinda aka bada rahoto cewa cutar ta kashe mutane uku.

Cutar Kwalera, cutar ce dake kama mutum ta wurin ruwan sha da abinci wanda ke shafar bayan garin mutane. Cutar na kai ga gudawa, karewar ruwan jiki da mutuwa, idan ba’a samu shan magani da sauri ba.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG