Wannan shine irin rudanin da ya baibaye cibiyar agajin gaggawa na asibitin kwararru dake Yola fadar gwamnatin jihar Adamawa, saa guda bayan wani harin bomb da aka kai a babban kasuwar Jimeta da musalin karfe7:15 na yammacin ranar alhamis, na iske mutane kwance kan siminti sharba-sharba kwance cikin jinni sakamakon raunuka da suka samu yayin da jamiaanasibitin keta kai kawo na kokarin ceto rayukan su.
Mallam Sini wani dan kasuwa ne da bomb din ya tashi a gaban shagon sa kuma ake wa jinya na raunuka da yasamu a kafar sa ta dama, ya shaida mani cewa yaga wau samari biyu na cacar baki kafin tashin bomb din.
‘’Sunana Senitari,bomb shin yaya abin ya faru?
Ni dai naga yara suna fada ne daga cikin fada ne sai suka taru suna cikin fada din sai kawai wani abu ya tashi, ina tsaye a gaban shago na sai wani abu yazo ya same ni a kafafu na’’
Mallam Saadu bello na hukumar kai doki na gaggawa na hukumar NEMA ya shaida mani ta wayan tarho cewa gawarwaki 27 ne aka kwashe daga harabar.
‘’Alhamdulillahi abubuwa sun lafa kuma an samu shiga wurin an cire wadanda abin ya rutsa dasu, wadanda dai muka iya fito da gawarwakin su 27 ne wadanda suka mutu’’
Jamiin hulda da jamaa na rundunar yan sanda na jihar Adamawa dsp Abubakar Usman ya tabbatar da faruwar al’amarin yace tuni jamiaan sa sun samu isa harabar.
‘’Ba shakka an samu tashin bomb jamiian mu sun samu isa wurin basu cikkaken rahoto ba tukunna’’
Shima sabon gwamnan jihar na Adamawa Mr Jibrin Bidowa wanda ya ziyarci asibitin cikin kaduwar hankali da juyayi domin ganewa idanun sa da kuma jajantaw wadanda bomb din ya rutsa dasu ya yaba wa likitocin na irin kokarin da suke yi koda yake bai iya yin dogayen kalamai ba.
Dr Asibitin kwararru na Yola Dr Bala yace dakunan jinya dake asibitin suncika makil da jamaa wadanda harin ya rutsa dasu kuma suna bakin iya kokarin su wajen yi musu jinya.
‘’Muna da ward-ward har guda 8 duka sun cika da mutane muna musu jinya, motocin guda 3 duka suna taimakawa suna dibar mutane suna kaiwa FMC suna taimakawa, kuma kamata yayi hatta masu asibitoci masu zaman kansu da suke kusa kamata yayi su bude su taimaka wa mutane a yanayin da muke ciki yanzu, kuma magungunan da yakamata mu bayar muna dibowa daga sito din mu mana bayar wa, kawo yanzu dai bamu da wani babban matsala.
Hakimin Jimeta Alhaji Baba Paris yace harin Bomb din ba zata yazo lokacin da mutane suke dauka harin boko haram ya lafa a jihar ta Adamawa.
‘’Wannan abu ya girgiza mu kwarai da gaske domin bamu taba tsammanin cewa irin wannan zai faru damu ba lokacin da ake tsananin wannan abubuwa ALLAH ya kare mu, abu yazo daga karshe kuma munzo mu samu wannan abu ba dadi.
Your browser doesn’t support HTML5