Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

FIFA: Amurka Ta Fitar da Takardun Bayanan Cin Hanci


Charles Blazer na FIFA wanda ya amsa laifin cin hanci
Charles Blazer na FIFA wanda ya amsa laifin cin hanci

Wani kotun Amurka ta fitar da takardun bayanan cin hanci da aka zargin wasu manyan hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA

Takardun bayanai daga wata kotun Amurka sun nuna cewa manyan ‘yan kwamitin koli na hukumar kwallon kafa ta duniya ko FIFA sun amsa laifin cin hanci dangane da shirye-shiryen wasannin shekarun 1998 da 2010.

Su jami’an sun amince da abun da suka yi a watan Nuwamban shekarar 2013 biyo bayan binciken kwakwaf da mahukuntan Amurka suka yi.

Charles Blazer dan asalin Amurka wanda ya kwashe shekaru 20 yana cikin manyan jami’an FIFA ya amsa a asirce aikata zarge-zarge 10 da aka tuhumeshi dasu a Birnin New York. Amma ya amsa ne a asirce

Amincewarsa tana cikin wata yarjejeniya ce da ya cimma da jami’an Amurka masu gabatar da kara domin ya samu sassauci.

Blazer ya gayawa alkali a Amurka cewa shi da wasu manyan jami’an FIFA sun karbi cin hanci akan baiwa kasar Faransa izinin gudanar da wasan cin kofin kwallon kafa na duniya a shekarar 1998.

Jami’an Amurka sun kara da cewa Blazer yace ya yadda ya karbi cin hanci akan gudanar da wasan shekarar 2010 da aka baiwa Afirka Ta Kudu.

Haka jiya Laraba ‘yansandan kasa da kasa sun bada takardar sammacin manyan jami’an FIFAsu biyu da wasu guda hudu akan almundahana da cuku-cuku.

Mutanen ana iya kamasu ko ina a duniya

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG