Majalisar Dattijai ta zartas da kudurori 46 a zaman majalisar ranar Laraba, aikin da kusan majalisar take yi a shekara daya.
Sai dai a cikin dokokin duka babu dokar da zata kayyade irin akace aikacen kamfanin man fetur ta kasa da aka fi sani da NNPC, dokar da aka yiwa lakabin PIB.Idan da har dokar ta sami amincewa da a jin zata kawo karshen zargin sama da fadi da dukiyar jama'a a kamfanin.
Rashin amincewa da dokar ya janyo gunani da surutai daga wakilan majalisar, har ta kai ga shugabanta David Mark ya tsawatar. Ya gayawa takwarorinsa ceewa idan basu gamsu da hukuncin da ya yanke kan kudurori da aka amince dasu ba, suna iya sake gabatar da bukata a zaman majalisar ranar Alhamis din nan.
Dan majalisar Etta Enen, duk da yawan kudurori da suka maince dasu har 46 duk zasu kasance a banza idan doka mai tasiri kan harkokin kamfanin NNPC bata ciki.
Ga karin bayani.