Wasu tagwayen hare-haren kunar bakin wake a Kabul, babban birnin kasar Afghanistan, sun yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 26, ciki har da ‘yan jarida 9. Wasu su 50 kuma sun jikkata, ciki har da ‘yan jarida 5.
Kungiyar ISIS, ta kamfanin dillancin labaranta, ta dauki alhakin kai harin, mafi muni da aka taba gani akan ‘yan jarida a Afghanistan.
Hukumar da ke sa ido akan ‘yan jarida a Afghanistan da ake kira AJSC a takaice, a yayin da ta ke tabbatar da mummunan harin da ya shafi ‘yan jarida, ta yi Allah wadai da harin da kakkausan lafazi.
Wasu mata biyu ‘yan jarida, ciki har da Maharram Durrani daga RFE/RL, na daga cikin wadanda su ka mutu. Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya tabbatar da mutuwar babban mai daukar masu hotuna a Kabul, Shah Marai. Wasu ma’aikatan RFE guda biyu, Abdullah Hananzai da Abawoon Kakar, na cikin wadanda suka mutu.
Hukumomin Afghanistan da wadanda su ka shaida lamarin sun ce an fara harin ne da sassafe, yayinda mutane ke yawan zirga-zirga, a lokacin ne wani dan kunar bakin wake akan babur ya tada nakiyarsa a kusa da ofishin leken asirin kasar.