Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Hanyar Zaman Lafiya a Yankin Koriya


Shugaba Kim Jong Un da Shugaba Moon Jae-in
Shugaba Kim Jong Un da Shugaba Moon Jae-in

A wani abu mai kama da almara, ana ta ganin alamar yiwuwar a samu zaman lafiya mai dorewa a yankin ruwan Koriya.

Masu fada a ji a Amurka na dada nuna kwarin gwiwar cewa zaman doya da manjar da aka shafe shekaru gommai ana yi a yankin ruwan Koriya na dosar zuwa karshe fiye da yadda aka taba gani.

“Ba na jin wargi ya ke yi, sam ba na jin wargi yak e yi,” abin da Shugaban Amurka Donald Trump ya fada kenan a Fadar Shugaban kasa ta White House, lokacin da aka masa tambaya jiya Jumma’a kan Shugaban Koriya Ta Arewa Kim Jong Un da kuma ganawar da ake kyautata zaton za su yi.

“Ba a taba samun irin wannan cigaba a batun ba,” a cewar Trump, yayin da ya ke tsaye ganga da Shugabar Jamus Angela Merkel.

Trump ya kara da cewa Amurka za ta tsai da lokacin ganawar ba da dadewa ba, to amma bai fayyace ba, ya kara da cewa jami’an gwamnati na nazarin wurare biyu zuwa uku da za a yi taron da ake dokin ya faru tsakaninsa da Shugaban Koriya Ta Arewa Kim Jong Un zuwa karshen watan Mayu ko kuma a farko-farkon watan Yuni.

Tun da farko a jiya Jumma’a Kim ya kasance Shugaban Koriya Ta Arewa na farko da ya taba taka kasar Koriya Ta Kudu, bayan da ya ketara kan iyaka ya sha hannu da Shugaban Koriya Ta Kudu Moon Jae-in.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG